Jerin Sunayen Manajojin Kwallon Kafa Da Suka Yi Fice A Wannan Karnin

Zlatan Ibrahimović dan kasar Sweden

A halin da ake ciki, Zlatan Ibrahimović ya ayyana yin ritaya daga wasan kwallon kafa na kwararru, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da magoya bayan klub din AC Milan a karshen wasan da suka yi da klub din Hellas Verona a San Siro

Na farko shi ne dan kasar Sifaniya, wanda yayi fice a fannin kyakkyawan tsari da iya mallakar kwallo a lokacin da ake murzawa.

Ya taba zama manajan klub din Barcelona, Bayern Munich da kuma Manchester city. Tun bayan dawowarsa Man City, ya mamaye harkar kwallo a bangaren premier inda ya lashe kofunan premier da wasu kofunan cikin gida, ya kuma kawo wani sabon salon kai farmaki a harkar kwallo.

A halin yanzu yana shirin cimma nasarar daukar kofin zakarun Turai a fafatawar karshe tsakaninsa da klub din Inter Milan a karshen mako.

Pep Guardiola- Champions League

Na biyu kuma shi ne Jose Mourinho, wanda yayi fice a fannin samar da yanayi a fagen murza leda sannan kuma da dabarun buga kwallo.

Mourinho ya sami nasarori a kewayen nahiyar Turai, ya kuma sami lambobin yabo a klub-klub din da suka hada da Chelsea, Inter Milan, Real Madrid, Manchester United, Porto, da kuma Roma.

Jose Mourinho,

Sai na uku tsoho mai ran karfe, Sir Alex Ferguson. Duk wanda ji wannan sunan sai ya tuna da klub din Manchester United da ake kira Man U a takaice. Ferguson ya gina wata daula da ta dade a harkar kwallon kafa.

Ya ci kofin premier har sau goma sha uku sannan ya sami matsayin manajan da ya fi samun yabo a rukunin premier na kasar Ingila, ya kai klub din Man U har ya lashe kofin zakarun Turai a shekarar 1999 da kuma 2008.

Alex Ferguson

Carlo Ancelloti, kocin Klub din Real Madrid, yana daga cikin manajojin klub din kwallon kafa da suka yi fice.

Ancelloti ya samu nasarori a shiyyar kasar Turai kuma ya zama manaja a klub-klub da yawa ciki har da AC Milan, Chelsea, Paris Saint-Germain, Real Madrid da Bayern Munich. Sau hudu Ancelloti na daukar kofin zakarun Turai.

Carlo Ancelotti

Na biyar kuma shi ne Zinedine Zidane, tsohon manajan klub din Real Madrid, wanda ya dauko kofin zakarun Turai sau uku a jere daga shekarar 2016 zuwa 2018.

Zidane ya dauko kofuna da suka hada da na Laliga har sau biyu, da kuma na hukumar kwallon duniya na klub-klub, nan ma sau biyu. Zidane mutum ne mai natsuwa da basirar sarrafa ‘yan wasan kwallo wanda suka goge.

Zinedine Zidane

A halin da ake ciki, Zlatan Ibrahimović ya ayyana yin ritaya daga wasan kwallon kafa na kwararru. Ibrahimović ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da magoya bayan klub din AC Milan a karshen wasan da suka yi da klub din Hellas Verona a San Siro inda suka sami nasara a kan Hellas Verona da ci 3 da 1 a karshen mako.

Zlatan Ibrahimovic

Shekarun Ibrahimović 41 a yanzu. Ya buga wa manyan klub-klub din kasashen Turai da suka hada da Juventus, Paris Saint-Germain, AC Milan, Inter Milan, Manchester United, Barcelona da kuma Ajax wasa sosai.

Shi kuma Karim Benzema, ya bayyana barin klub din Real Madrid a karshen mako zuwa klub din Al ittihad na kasar Saudiyya inda ya sami kwantiragi na tsawon shekaru uku. Benzema ya shafe tsawon shekaru 14 a Laliga.

BENZEMA

Saurari rahoton Abdulwahab Muhammed:

Your browser doesn’t support HTML5

Jerin Sunayen Manajojin Kwallon Kafa Da Suka Yi Fice A Wannan Karnin