A yau Lahadi shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fadawa dakarun Amurka a sansanin Yokota na kasar Japan cewa, “Babu wani mutum, ko shugaban mulkin kama karya, ko wata gwamnati… da zata yiwa Amurka kallon raini.”
Furucin shugaba Trump ya zo ne a farkon ziyarar da ya fara ta kudan mako biyu a Asiya, ziyarar da ake sa ran zata mayar da hankali kan Koriya ta Arewa.
Yawancin maganganun da yayi, yayin da yake jawabi ga sojojin Amurka, za a iya kallonsu a matsayin hannunka mai sanda ga kasar da ta zama saniyar ware a duniya. Trump fadawa sojojin Amurka cewa yace “ku babbar barazana ne ga azzalumai da masu mulkin kama karya wadanda suke cin zarafin mutanen da basu ji ba basu gani ba.”
Akan hanyarsa ta zuwa Japan, shugaba Trump yayi magana da manema labarai lokacin da yake shirin hawa jirginsa, inda wakilin Muryar Amurka Steve Herman ya tambayeshi ko yana da wani sako ga mutanen Koriya ta Arewa. sai ya ce “ina tunanin mutanen kirki ne, masu kokarin aiki. Mutanen kirki ne ba kamar yadda duniya ke ‘daukarsu ba. Ina fatan komai zai tafi dai-dai ga kowa.”
Trump kuma ya nuna cewa zai gana da shguaban kasar Rasha Vladimir Putin a bayan fagen taron bunkasa tattalin arzikin yankin Asiya da Pacific da za ayi a Philippines.
Shguaba Trump dai ya isa kasar Japan bayan da ya yada zango a jihar Hawaii inda ya ziyarci tsohon jirgin yakin ruwan Amurka na USS Arizona dake a tashar Pearl Harbor, gurin da Japan ta kaiwa harin ba zata a shekarar alif 941, harin da ya jefa Amurka cikin yakin Duniya na biyu.