Jiya Lahadi Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da 'yan matan Chibok 82 dalibai, wadanda masu tsattsauran ra'ayin nan na Boko Haram su ka sace su, bayan da aka sako su ranar Asabar a arewa maso gabashin Najeriya mai fama da hankali.
WASHINGTON D.C. —
Faifan bidiyon ganawar a Abuja, babban birnin kasar, na nuna Shugaba Buhari na jawabi ma galabaitattun 'yan matan, ya na ce masu, "ba wani dan adam din ya kamata ya dandana irin wannan masifar!" Ya kuma yi alkawarin cewa kai tsaye Fadarsa za ta sa ido kan wadanda za su kula da 'yan matan.
Zuwa jiya Lahadi babu cikakken bayanin yadda 'yan matan su ka samu kubuta. To amma sakin nasu ranar Asabar ya biyo bayan tattaunawa mai tsawo da wakilan Boko Haram; tattaunawar da ta hada da batun sakin 'yan matan a madadin sakin wasu kwamandojin Boko Haram.
Kafar labarai ta Associated Press ta fadi da safiyar jiya Lahadi cewa an sako kwamandojin Boko Haram biyar a madadin 'yan matan.