Jawabin Sabon Shekara: Za Mu Aiwatar Da Sabon Albashin Ma’aikata - Shugaba Tinubu

Bola Tinubu

A jawabinsa na sabuwar shekara na farko tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi ga al’ummar kasar, inda ya sanar da fara aiwatar da sabon albashin ma’aikata na kasa a cikin sabuwar shekara.

A jawabinsa na sabuwar shekara na farko tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi ga al’ummar kasar, inda ya sanar da fara aiwatar da sabon albashin ma’aikata na kasa a cikin sabuwar shekara,

Shugaban ya kuma yi tsokaci kan kalubalen da aka fuskanta a shekarar da ta gabata tare da bayyana tsare-tsaren gwamnatinsa na gaba.

Shugaba Tinubu ya fara ne da nuna godiya ga ‘yan Najeriya, inda ya jaddada mika mulki cikin lumana wanda ya zama wani babban abin alfahari ga dimokradiyyar kasar a cikin shekaru 24 na mulkin farar hula ba tareda tsangwamar soji ba.

Ya amince da kalubalen da aka fuskanta a shekarar 2023 da kuma amanar da al’ummar Najeriya suka ba shi na inganta tattalin arziki, da inganta tsaro, da kuma ciyar da kasa.

Da yake karin haske kan tsauraran matakai da aka dauka a cikin watanni bakwai da ya yi yana mulki, Shugaba Tinubu ya yi tsokaci kan cire tallafin man fetur da garambawul a tsarin musayar kudaden waje, yana cewa,

“A cikin watanni bakwai da suka gabata na gwamnatinmu, na dauki wasu matakai masu matukar wahala amma kuma duk da haka sun zama dole don ceto kasarmu daga bala'in kasafin kudi.

"Ɗaya daga cikin waɗannan matakai shine cire tallafin man fetur wanda ya zama wani nauyi mai wuyar gaske ga kasarmu fiye da shekaru arba'in.

A daya bangaren kuma shi ne kawar da wahalhalun da wasu tsirarun mutane suka yi a kan tsarin mu na musayar kudaden waje wanda kawai masu hannu da shuni ne kawai ke amfana daga cikinmu. Babu shakka, daukar waɗannan matakai guda biyu sun kawo rashin jin daɗi ga mutane, iyalai da kasuwanci.”

Da ya ke jawabi game da tsadar rayuwa, hauhawar farashin kayayyaki, da rashin ayyukan yi, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa al’ummar kasar cewa wannan lokaci da ake ciki na wahala na wucin gadi ne.

Ya yi kira ga ’yan kasa da su ci gaba da jajircewa wajen gina ingantacciyar Najeriya, yana mai jaddada gwamnati zata tabbatar ta jaddada imanin ‘yan kasa wajen shawo kan matsaloli da al'umar kasa ke fama da shi kaman kalubalen zamantakewa, walwala, tattalin arziki da tsaro.

Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin samar da wutar lantarki akai-akai da irin matakan da gwamnati ke dauka domin tabbatar da haka,

“A watan Disambar da ta gabata a lokacin taron COP28 a Dubai, ni da shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, mun amince kuma mun himmatu ga wata sabuwar yarjejeniya don aikin samar da wutar lantarki na Siemens Energy wanda a ƙarshe zai haifar da ingantaccen wutar lantarki ga gidajenmu da kasuwancinmu, wanda hakan na ƙarƙashin yunkurin gwamnati tun shekarar 2018 da aka fara.

"Gwamnatina ta fahimci cewa babu wani sauyi mai ma'ana na tattalin arziki da zai iya faruwa ba tare da tsayayyen wutar lantarki ba. ” inji shugaba Bola Tinubu.

Ya sanar da shirin sake fara tace man fetur a cikin gida na matatar mai ta Fatakwal da kuma sabuwar matatar mai ta Dangote da ke Legas.

Ya kuma tabo batun noma inda yace, “domin tabbatar da samar da abinci, za mu kara himma wajen noma hekta dubu 500,000 na gonaki a fadin kasar nan domin noman masara, shinkafa, alkama, gero da sauran kayan amfanin gona. Mun kaddamar da noman rani da fili mai fadin hekta dubu 120,000 a jihar Jigawa a watan Nuwamban da ya gabata a karkashin shirinmu na bunkasa noma a kasa.”

Shugaban ya yi alkawarin yaki da matsalolin da ke kawo cikas ga kasuwanci tare da maraba da saka hannun jari na gida da waje. Ya zayyana fannoni takwas da suka fi ba da fifiko a cikin kasafin kudin shekarar 2024, da suka hada da tsaron kasa, samar da ayyukan yi, daidaiton tattalin arziki, inganta yanayin zuba jari, bunkasa jari, rage talauci, da tabbatar da zaman lafiya.

Da yake rufe jawabinsa, Shugaba Tinubu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada kai don samar da zaman lafiya, ci gaba, da zaman lafiyar kasar.

Shugaban ya kammala da yi wa daukacin ‘yan Nijeriya fatan alheri da ci gaba a shekarar 2024, tare da rokon Allah ya albarkaci tarayyar Nijeriya.

Tambayar ‘yan Najeriya ba ta wuce har tsawon yaushe za’a dauka cikin irin wannan yanayi na wahala kuma har zuwa wani lokaci dadin zai zo?

A saurari rahoton Umar Farouq Musa:

Your browser doesn’t support HTML5

Jawabin Shugaba Tinubu Na Sabuwar Shekara.mp3