Jawabin Janar Buratai Ya Janyo Cece-Kuce Tsakanin Masana Tsaro

Janar Tukur Buratai

Babban hafsan hafsohin sojojin Najeriya, janar Tukur Buratai, ya yi jawabi a babban birnin Abuja, wajen wani taron bita da aka shiryawa dakaru, jawabin da ya janyo cece-kuce.

Da yake jawabin Janar Buratai ya ce “rashin kwazo da rashin azama wajen yin fada, na wasu daga cikin hafsoshi da sojoji na daga cikin abubuwan dake haddasa musu koma baya a fafatawar da ake yi yanzu.”

Janar Buratai, wanda ya ce ko da baya ga zagon ‘kasa da ake yi musu, akwai kuma tabbatattun shaidu dake nuna koma bayan da ake fuskanta a baya-bayan nan nada alaka da rashin kishin ‘kasa da kuma rashin kishin aikin soja.

Tuni dai wannan jawabi na janar Buratai ya haddasa cece-kuce tsakanin masana tsaro da kuma tsaffin jami’an tsaron.

Dakta Kabiru Adamu, na daga cikin wadanda ke ganin rashin dacewar wannan jawabi na Buratai, inda ya ce ko da kuwa akwai matsalar tsaro bai kamata ba hafsan Soja ya fito ya yi irin wadannan kalaman ba.

Sai dai kuma tsohon hafsa a rundunar sojan Najeriya, majo Shu’aibu Bashir Galma, na ganin kalaman da janar Buratai ya yi na bisa hanya.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Jawabin Janar Buratai Ya Janyo Cece-Kuce Tsakanin Masana Tsaro - 2'59"