Jaruman Kannywood Sun Fara Karbar Allurar Riga-kafin COVID-19

Ali Nuhu, hagu da Aminu Shariff Momo, dama (Hoto: Instagram)

Wasu daga cikin jaruman Kannywood sun fara yin allurar riga-kafin COVID-19 yayin da ake ci gaba da aikin yin allurar a sassan Najeriya.

Jaruman masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood da ke arewacin Najeriya, sun fara bin sahun mutanen da ke zuwa yin allurar riga-kafin cutar korona.

Daga cikin jaruman akwai Aminu Shariff Momo da Rashida Mai Sa’a, wadanda suka wallafa hotunan lokacin da ake musu allurar a shafukansu na Instagram.

“Na karbi allurata a yau, tana da inganci kuma ba ta tattare da wani hadari.” In ji Momo.

"A yau, na karbi allurar Oxford AstraZeneca. ku je a yi muku ta ku yanzu" In ji Ali Nuhu.

Ita kuwa jaruma Rashida Mai Sa’a cewa ta yi, “mun karba, mu ma a kula da mu,” inda bayan da aka yi mata allurar ta kuma yi kira ga gwamnati da ta samar da tsaro a kasar.

“Ya kamata a zuba mana matakan (jami'an) tsaro su kula da rayuwarmu, tun da an mana allurar korona, a saka mana matakan tsaro daga masu garkuwa da mutane, kowa ya yi bacci a gidansa.” Rashida ta ce.

A ‘yan makonnin da suka gabata aka fara aikin yin allurar nau’in AstraZeneca a wasu sassan Najeriya yayin da jihar Kano da ke arewa maso yammacin kasar, ta fara yi wa al’umarta a makon da ya gabata.

A baya-bayan nan hukumomin Kano suka yi korafin cewa jama’a ba sa fita domin karbar allurar a daidai lokacin da was uke nuna shakku kan riga-kafin.

Hakan na faruwa ne yayin da allurar AstraZeneca take fuskantar suka a sassan duniya kan cewa tana haifar da daskarewar jini.

Ko da yake, hukumomin lafiya na duniya sun sahale a ci gaba da yin amfani da ita suna masu cewa alfanunta ya fi illar da take haifarwa.