Fim din ‘Yellow Paper’ fim ne da ya tara jarumai da dama daga sassan Afrika, wanda yayi duba da yanayin zamantakewa tsakanin al'ummar Afrika, kuma wata dama ce babba da na samu a matsayina na jarumi wanda na fito a cikin wannan fim din acewar Nuhu Abdullahi.
Ya kara da cewar fim din 'Yellow Paper' ya duba matsalolin 'yan gudun hijira, kana suka waiwayi matsalolin Afrika a dunkule. An kuma shirya fim din ne a harshen Turanci da kuma Faransanci.
Ku Duba Wannan Ma Zainab Indo Mie: Zata Dawo Duniyar Fina Finai Bayan Hutun Shekaru 5Masu shirya fim din 'Yellow Paper' sun zagaye ilahirin nahiyar Afrika, sannan suka shiga kowacce masanaantar shirya fina-finai inda suka dauki jarumi guda daya a kowacce masanaanta domin fitowa a fim din, Nuhu Abdullahi dai ya fito ne a matsayin kanin wani maikudi, aka kuma yi amfani da wata 'yar jarida domin a kwace masu dukiya.
Nuhu Abdullahi, ya ce masu shirya fim din sun nuna 'kwarewarsu ta kololuwa sannan sun dauki tsawon lokaci wajen shirya fim din, sun yi bincike da kuma zuba jari mai yawa da ya dauki nauyin shirya fim din 'Yellow Paper'.
Daga cikin darussan da Nuhu ya dauka shine suna bawa aiki muhimmanci, tare da mutunta dukkanin jaruman da suka dauko wajen nuna daidaito tsakanin manya da kuma kananan jaruman nahiyar Afrika.
Your browser doesn’t support HTML5