Sana’ar kayan ado na mata wato kayan kyalekyale, sana’a ce da ta ja hankali domin a yanzu mafi yawan kudade na hannun mata kuma a kullum mace mai son kwalliya ce da son ado, inji malama Maryam Saleh Yusuf.
Matashiyar ta bayyana cewa ta fara sana’a ne tun tana aji na biyu a jami’a a lokacin da take karantun kwas din Business Admin, sakamakon ita mace ce mai son kwalliya, dan haka ta fara sana’a ne ta hanyar tallata hajatar ta tsakanin kawayenta ‘yan makaranta.
Maryam kan tallata kayanta ne ta hanyar kafar sadarwa irinsu Instagram da whatsapp, inda mafi yawa ta kan samu masu bukata su aika da kudinsu sannan na tura masu kayan.
Kowacce sana’ar hannu na dauke da kalubale, kuma duk macen da zata fara sana’ar hannu lallai sai ta sanyawa ranta cewar za’a karbi kayanta bashi kuma ba dukkanin wadanda suka karbi bashi bane zasu biya.
Malama Marayam, ta ce a zamanin nan da ake ciki dole mace ta zamo mai dogaro da kai da jajircewa wajen neman nata na kanta sannan ko da mace na karatun boko yana da kyau tana da sana’ar hannu.
Facebook Forum