Janye Sojojin Amurka Daga Syria Babbar Barazana Ce Ga Israi'la

Shugaba Donald Trump

Biyo bayan ganawaa da sanata Linsey Graham yayi da Shugaba Donald Trump, ya ce yana da kwarin gwiwa cewa zai dakatar da aniyarsa ta janye sojojin Amurka daga Syria, wanda hakan zai baiwa Iran damar ci gaba da yiwa Isra'ila Barazana.

Wani babban dan majalisar dattawan Amurka na jam'iyyar Republican ya fada a jiya Lahadi cewa, ya yi wata ganawa da shugaba Donald Trump, a fadarsa ta White House, inda ya tabbatar da aniyarsa ta murkushe kungiyar ISIS koda kuwa ya janye sojojin Amurka daga kasar Syria.

Sanata Lindsey Graham, ya yi kashedi cewa janye baki dayan sojojin Amurka daga Syria babbar illace ga tsaron kasa, kuma zai ba kungiyar ta IS damar gina kanta.

Sannan kuma hakan yaudara ce ga mayakar Kurdawa da Amurka ke marawa baya ta YPG da su ke yaki da ragowar ‘yan kungiyar IS, haka zalika janye sojojin zai baiwa Iran damar ci gaba da yiwa Isra’ila barazana.

A wata hirar ta talabijin da safiyar jiya Lahadi, Graham ya ce zai fadawa Trump ya saurara da batun janye sojojin da ya sanar a farkon wannan wata, lamarin da yasa mutane da dama su ka rika Allah wadai.

Koda yake yakan kalubalanci wasu manufofin Trump a kan harkokin kasashen waje, duk da haka Trump abokinsa ne, kuma Graham yana kyautata zato ganawa da su ka yi da shugaban kasar zata yi tasiri.