T.Y Dajuma Ya Kalubalanci Shugaban Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan.

A daidai lokacin da yakamata a fara aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya, da manyan ‘yan takarar shugaban kasa suka sawa hannu, sai gashi rahotani na bayanin cewa wadansu daga yankin Niger Delta.

A daidai lokacin da yakamata a fara aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya, da manyan ‘yan takarar shugaban kasa suka sawa hannu, sai gashi rahotani na bayanin cewa wadansu daga yankin Niger Delta, Asari Dokubo da Tompolo, sun fito kafofin yada labarai sun cewa idan shugaba Goodluck Jonathan, bai ci zaben dake tafe ba lallai za’a yi yaki a Najeriya.

Alkaluma sun ruwaito cewa wannan batu ya tunzura tsohon shugaban rundunar sojojin Najeriya, Janar T.Y Dajuma, mai ritaya har ya fito fili ya kalubalanci fadar shugaban kasa, da ta kama wadannan mutane ta hukumta su.

Wannan furuci da janar T.Y Dajuma, yayi shine karo na farko da wani babba daga yankin arewa, yana tsawatawa a game da irin wannan munanan kalamai.

Mainasara Kogo Ibrahim, wani masani a harkar tsaro, siyasa da harkokin kasashen duniya, ya yaba da wannan yunkuri da Janar T.Y Danjuma, yayi, yace“ Na farko abune na a gode mashi kuma ko a gida idan aka kasance babu manya abubuwa su kan kasance sun tabarbare, wasu suna daukar kansu a matsayi suna sama da doka ko kuma sun fi karfin hukuma ta iya yi masu wani abu a Najeriya, wannan har ya zama al'ada, inda wasu ke bugun kirji suna ganin kamar su suna sama da sauran bangarorin kasar nan, kuma ba yau ne suka fara wannan abun ba, amma kasancewa manyan kasa suyi shiru basu cewa komai ba, saboda haka wannan abune na a yaba mashi, da muna dauka cewa manya gabadaya, su sama manyan zane kwai domin sun kasa fitowa suyi wannan maganan.”