Janar Tiani Ya Soke Wa Hadiman Bazoum Takardun Shaidar Zama 'Yan Kasa

Janar Abdouramane Tchiani

Ana zarginsu da yada bayanan tada zaune tsaye da kulla makarkashiya da cin amanar kasa da ma bada gudumowa a yunkurin katse hanzarin rundunar tsaron kasa da nufin haddasa cikas wa aiyukan tsaro.

A wani abin da aka kira matakin wucin gadi, hukumomin mulkin sojan Nijar sun ba da sanarwar soke wa wasu mukarraban hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum takardun shaidar zaman ‘yan kasa a bisa zarginsu da aikata jerin wasu laifuka masu nasaba da yi wa tsaron kasa barazana da cin amanar kasa da dai sauransu.

Haka kuma ana zarginsu da yada bayanan tada zaune tsaye da kulla makarkashiya da cin amanar kasa da ma bada gudumowa a yunkurin katse hanzarin rundunar tsaron kasa da nufin haddasa cikas wa aiyukan tsaro.

Mutanen da sanarwar sakatariyar gwamnatin Nijar ta ayyana a matsayin wadanda shugaban gwamnatin mulkin soja Janar Abdourahamane Tiani ya kwace wa takardun zama ‘yan kasa a karkashin dokar yaki da ta’addanci ta ranar 27 ga watan Agustan 2024 sun hada da tsohon minista Rhissa Boula da Pagoui Hamidine Abdou da Amadou N’gade Hamid da Abdoukader Mohamed.

Sai Abou Mahamadou Tarka da Daouda Djibo Takoubakoye da Karingama Wali Ibrahim da Harouna Gazobi Souleymane da Moussa Moumouni wadanda dukkansu kusoshin fadar shugaban kasa ne a zamanin shugaba Mohamed Bazoum, matakin da tuni ya fara daukan hankulan ‘yan kasa.

Kawo yanzu ba wani martani daga bangaren mutanen da abin ya shafa , dukkansu na hijira a kasashen waje inda suke caccakar manufofin CNSP ta kafafen sada zumunta.

Hasali 1 daga cikinsu wato Rhissa Boula ya sanar da kafa kungiyar ‘yan tawaye don gwagwarmaya da makamai da nufin mayar da Nijar kan tafarkin dimokradiya.

A washegarin kirkiro da wannan doka Kungiyar Transparency internatinal da Human Rigths Watch sun bukaci hukumomin Nijar sun janye kudirin da suka ayyana a matsayin wanda ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Saurari cikakken shirin Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Janar Tiani Ya Soke Wa Hadiman Bazoum Takardun Shaidar Zama 'Yan Kasa