Farfesa Ango Abdullahi, shugaban kungiyar dattawan arewa, yace kungiyar na goyon bayan dan takarar shugabancin kasa da jamiyyar, APC, ta tsayar janar Muhammadu Buhari.
Farfesan ya bayana haka ne a wani hira da wakilin muryar Amurka, Isa Lawal Ikara, inda yake cewa alama ta nuna cewa hankali ya fara sauka a koina a kasar cewar an gaji da wannan tafiyar lokaci yayi da za’a canja wannan mulki, wanda yake ya kasa.
Dangane da kungiyar dattawan da Tanko Yakasai, kewa shugabanci kuwa Farfesa Ango Abdullahi cewa yayi, “Tunda farko munyi Magana akanta, ita ‘yar tallace kuma ana biyanta ladan tallar da take yi, jama’a sune alkalai, su sun ce sun yarda arewa ta samu mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, mu kuma mun ce shugaban kasa mu keso kuma ba’a bamu shugaban kasa a jamiyyar sub a saboda haka bamu tare dasu.”
Ya kara da cewa” kuma kowa ya sani cewa su Tanko Yakasai an kafa sune saboda wannan aiki nay a za’a yi a tabbatar da cewa an samu mataimakin shugaban kasa a arewa toh mu Northern Elders Forum ba mataimakin shugaban kasa mike nema ba, muna neman shugaban kasa ne shine banbancin mu dasu tun daga farko har zuwa yanzu, domin muna jira muga irin tallar da zasu yi muga kuma wanene mai saye a arewa.”
Your browser doesn’t support HTML5