Hadaddiyar kungiyar lafiya reshen jihar Kaduna, tace ta shirya fara wani yajin aiki da karfe goma sha biyu na daren Lahadi, matukar dai Gwamnatin tarayya bata biya mata bukatun ta ba.
Komrade, Ahamed Mairiga, shine shugaban kungiyar Malaman tsafta, a jihar Kaduna, kuma daya daga cikin ‘ya’yan hadaddiyar kungiyar ma’aikatan lafiya a jihar, ya umarci ‘ya’yan kungiyar cewa idan har bazu ji komai bat oh tabbaci hakika daga daren lahadi kowa yayi zaman sa a gida.
Ita kuwa shugaban hadaddiyar kungiyar ma’aikatan lafiya ta jihar Kaduna, Cecilia Musa, cewa tayi kungiyar a shirye take ta janye yajin aikin da zarar Gwamnatin tarayya ta cika masu bukatunsu.
Ta kara da cewa tilas ce zata sa su yin yajin aikin ba wai don suna son ba don tausayawa jama’ar da rajin aikin zai shafa masamman marasa lafiya, ta na mai cewa kotu ta riga ta yanke hukunci Gwamnati ya rage ta zartar da hukuncin kotu.
Dama dai sauran takwarorin kungiyar ta wasu jihohi tuni suka fara yajin aikin abunda yasa uwar kungiyar ta kasa ta bukaci reshen kungiyar na Kaduna cewa tabi sauran jihohin.