A binne marigayin ne kusa da kakanninsa a hubbarin sheik Usman bin Fodiyo dake Sokoto. Farfesa Sambo Wali Jinaidu, shine shugaban kwamitin bada shawarwari akan lamurran addini na fadar mai alfarma sarkin musulmi. Wanda kuma yayi aiki tare da marigayi, yace magariyin yayi rayuwa mai albarka, kuma ya taimaka sosai wajen harkar addini.
Rasuwar Alhaji Ibrahim Dazuki dai babban rashi ne ga al’ummar musulmi da ‘yan Najeriya baki ‘daya a cewar shugaban mabiya addinin Krista na darikar Katolika a yankin Sokoto, Rev Mathew Hassan Kuka, wanda shima ya halarci jana’izar marigayin.
An haifi sarkin musulmi na 18 Alhaji Ibrahim Dazuki ne a ranar 31 ga watan Disambar shekara ta 1923 inda ya kasance mutum na farko da ya hau kujerar sarkin musulmi daga gidan Buhari dan Shehu a rabar 1 ga watan Nuwambar shekara ta 1988 inda ya gaji sarkin musulmi Abubakar na 3. To sai dai gwamnatin mulkin soja a karkashin marigayi janal Sani Abacha ta cire Ibrahim Dazuki daga kan kujerar mulki inda aka kaishi Jalingo ta jihar Taraba domin zaman gudun hijira, kafin daga bisani aka dawo da shi Kaduna inda ya zauna har karshen rayuwarsa.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5