Gwamnati za ta bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya da wasu sassauƙan hanyoyin kuɗi ta hanyar kayan aiki daban-daban don yaƙar cutar ta mpox da kuma tallafawa abokan haɗin gwiwarta a Afirka ta hanyar haɗin gwiwar rigakafin GAVI, in ji kakakin.
Jamus tana da kusan allurai 117,000 na Jynneos, wanda sojojin Jamus ke tarawa tun bayan da Berlin ta sayo su a cikin shekarar 2022.
Kasar ta ce adana wani kaso na allurar, don kare hukumomi masu balaguro, in ji mai magana da yawun ma'aikatar tsaro a ranar Litinin. Ya kara da cewa dole ne a yanke shawara ta daban idan ana batun sake yin odar alluran rigakafi.
Hukumar lafiya ta duniya dai ta ayyana mpox a matsayin annobar gaggawa akan kiwon lafiyar jama'a a duniya bayan barkewar cutar a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo zuwa kasashe makwabta da wani sabon nau'in kwayar cutar ya bullo, “Clade Ib”, wanda ya haifar da damuwa kan yadda yake saurin yaduwar cutar.
-Reuters