Dubban ‘yan Nijar ne suka karbi gayyatar kawancen jam’iyun hamayya na FRDDR ranar Lahadi, wadanda suka taru a dandalin Place Toumo kafin su yi tafiyar da ta kaisu dandalin place DE LA CONCERATION dake kofar majalisar dokokin kasa, inda suka gudanar da gangami har ma shugabannin tafiyar a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Mahaman Usman suka yi jawabai.
Tsohon shugaban kasar ta Nijar ya gabatar da jawabi inda ya cacckaci gwamnatin mai ci, ya na mai cewa kasar na cikin mawuyacin hali ne sakamakkn rashin iya mulki, lamarin da ya haifar da tabarbarewar siyasa, tattalin arziki da kuma fannin al’adu.
Gwamnatin PNDS TARAYYA na mai ikirarin gudanar da manyan aiyuka a tsawon shekarun da shugaba Mahamadou Issouhou ya yi akan karagar mulki, sai dai shugaban jam’iyar ORDN TARMAMUWA kuma kusa a kawancen adawa na FRDDR Mamman Sani Adamou na cewa ayyukan ba ayi su don talaka ba.
Tsohon ministan harakokin wajen Nijar Ibrahim Yakuba, wanda jam’iyarsa ta MPN KISHIN KASA ta raba gari da gwamnati mai ci a watannin baya, ya halarci zanga-zangar ‘yan adawa, ya kuma bayyana ra’yinsa na cewa dole ne a tashi tsaye domin a takawa gwamnatin PNDD burki.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Your browser doesn’t support HTML5