Jam'iyyar PDP Ta Yi Hasarar Kujerar Kakakin Majalisar JIhar Taraba

Kotun daukaka kara ta tabbatar da cewa za a sake gudanar da zabe a wasu wurare 8 a bayan da ta soke kuri'un da aka ce an kadawsa Adiel Peter Diah a wadannan mazabun.

A bayan hukumcin da kotu ta bayar na soke zaben gwamna Darius Ishaku dan jam'iyyar PDP a Jihar Taraba, sai ga kotun daukaka kara a yanzu ta sake tabbatar da hukumcin da tun farko wata kotun zabe ta yanke game da kujerar kakakin majalisar dokokin jihar ta Taraba, Adiel Peter Diah.

A bayan hukumcin farkon ne sai kakakin majalisar dokokin ya garzaya kotun daukaka kara domin neman hana gudanar da wancan hukumcin da ya bukaci sake gudanar da zaben a wasu rumfunan zabe na mazabarsa.

A yanzu haka dai, dukkan jam'iyyun PDP da kuma APC a jihar ta Taraba sun fara cacar baki a kan wannan zaben da za a sake gudanarwa.

Shugaban jam'iyyar APC a Jihar Taraba, Alhaji Hassan Jika Ardo, yayi zargin cewa sun bankado wani yunkurin da PDP keyi na sayen kuri'u a wurare guda takwas da za a sake gudanar da zaben Mr. Adiel Diah.

Sai dai kuma Alhaji Abubakar Bawa na jam'iyyar PDP yayi watsi da wannan zargin, yana mai fadin cewa idan 'yan APC su na neman jama'a ne su je su nema ba wanda ya hana su, amma zarge-zarge marasa kan gado ba su ne zasu kawo musu kuri'a ba.

Rundunar 'yan sandan jihar Taraba ma ta ce a shirye take domin gudanar da wannan zabe wanda har yanzu ba a sanya ranar yi ba. Kwamishinan 'yan sanda a jihar ta Taraba, Alkali Sha'aba, yayi kira ga 'yan siyasa da su guji kalamun da zasu iya tayar da fitina.

Your browser doesn’t support HTML5

PDP Ta Yi Hasarar Kujerar Kakakin Majalisar JIhar Taraba - 4'23"