Jam’iyyar Mega Progressive People’s Party da aka fi sani da MPPP a takaice, ta shigar da karar hukumar zabe ta INEC da gwamnan jihar Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a gaban kotun zabe bisa zargin cewa ba a sanya sunayen ‘yan takararsu da da tambarin jam’iyyarsu ba a lokacin zaben ‘yan majalisun tarayya.
Karar wacce wasu ‘yan takara a jam’iyyar ta MPPP sukar shigar, na nema ne a soke zaben da aka yi a kuma gudanar da sabo.
Sauran wadanda aka shigar da kara akan su a gaban kotun korafin zaben, sun hada da Hon. Barau Jibrin da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, wadanda dukkaninsu ‘ya’yan jam’iyyar APC ne.
Hukumar zabe dai ta bayyana wadannan mutane a matsayin wadanda suka lashe zaben kujerun ‘yan majalisa masu wakiltar Kano ta Kudu da arewa.
“Mun kai kara ne bisa cire mu da aka yi a cikin masu takara na sanatoci guda uku da muka cike a jihar Kano, wanda muke bi-biyar kotu ta fitar mana da hakkin mu, mu ji dalilin da ya sa ita hukumar zabe ya sa ba ta bugo sunayenmu da na tambarin jam’iyyar mu ba.” In ji Shugaban jam’iyyar MPPP, reshen Kano, Alhaji Isa Nuhu Dan Fulani.
A cewar shugaban jam’iyyar, sun yi iya bakin kokarinsu su ja hankalin hukumar zabe cewa ba a saka sunayensu da tambarin jam’iyyarsu ba, amma abin ya cutura.
“Abin da ya sa muke so shi ne a rushe zabe, jama’ar da suke kokarin su zabe mu su jefa mana kuri’a, muma mu tabbatar mun ci ko ba mu ci ba, domin hankalin mu ya kwanta.” Dan Fulani ya kara da cewa.
Saurari wannan rahoto domin jin karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5