Yanzu gani ya kori ji musamman idan aka yi la'akari da matsalolin ambaliyar ruwan sama da karacin ruwan saman ga manoma a wasu sassa.
Yawan sare-saren bishiyoyi da zafin da ake fuskanta ya sa gwamnatoci sun fara daukan matakan da suka kamata saboda magance dumamar yanayin duniya.
Farfasa Ahmed Sadauki Abubakar shugaban cibiyar nazari akan matsalolin dumaman yanayi na yammacin Afirka yayi karin haske gameda matsalar da dumaman yanayi ke haifarwa a duniya. Dumaman yanayi ya shafi noma gaba daya, wato shuka da girbi. Ya shafi yadda ake tafiya da jiragen ruwa da na sama. Farfasa yace hatta lafiyar jikinmu dumaman yanayi ya shafeta.
Sare bishiyoyi ba tare da maye gurbinsu ba na daya daga cikin matsalolin dake haddasa kwararowar hamada. Saboda haka kamata yayi a daina anfani da itace ana dafa abinci to amma sai gwamnati ta tanadi wata wadatacciyar hanya. Idan an hana saran itace dole ne a ba mutane abun da zasu dafa abinci dashi.
Gwamnatocin kananan hukumomi da na jihohi da na tarayya ya kamata su killace wasu wurare inda zasu shuka bishiyoyi su kuma hana sare itatuwa a wuraren. Yin hakan zai hana kwararowar hamada.
Jiya aka tuna da ranar dumaman yanayin duniya domin jawo hankalin bil Adama akan mahimmancin daukan matakan da zasu rage matsalarsa.
Ga rahoton Babangida Jibrin.