Kwamitin gudanarwa na Jam’iyyar Democrat ya sanar da hukumar binciken manyan laifuka na kasar (FBI) cewa yayi nasarar tarwatsa wani yunkurin satan bayanai dake runbun adana bayanan masu jefa kuri’a.
Bob Lord babban jami’in tsaro na wannan kwamitin ya yi wa shugabanin jam’iya bayani akan wannan yunkurin da aka yi. Ya dai yi musu bayanin ne a wajen taro da aka yi jiya laraba a birnin Chicago.
Lord yace wannan yunkurin ya nuna a zahiri cewa a ko da yaushe akwai barazanar da ake huskanta musammam da yake ana dunfarar lokacin zaben rabin wa’adi, sai dai yace amma ba zasu yi kasa a gwiwa ba.
Sai dai dama tun a zaben shugaban kasa na shekarar 2016 ne ake ta samun gutsiri tsoma akan runbun tattara bayanai na Jamiyyar Democrat, lokacin da Rasha ta samu shiga cikin sa abinda ya haifar da Baraka tsakanin ‘yan takarar jamiyyar Democrat su biyu wato Hillary Clinton da Bannie Sanders. Rasha ta sha karyata wannan zargi.