Jami'iyyar ta musanta batun cewa zata ladaptar da Aisha Buhari bisa kalamunta maimakon hakan ma jam'iyyar tace tana goyon bayanta saboda ta fadi gaskiya
Sakataren tsare-tsaren jam'iyyar na jihar Ahmed Lawal yace dama ba tun yau ba ne suke son fadakar da shugaban kasa kan irin matsalolin da matar shugaban ta zayyana. Yace yakamata a zauna ne a tattauna. Yace ba'a shiga tsakanin miji da mata. Yace dama akwai wasu da suke zarginta wai tana hana ruwa gudu. Da kalamunta ta wanke kanta. Ta fadi gaskiya kuma ya kamata a duba a yi gyara.
Jam'iyyar tana bayanta dari bisa dari saboda haka batun labaptar da ita bai taso ba. Yace kada a manta Aisha ta yiwa jam'iyyar gwagwarmayar neman zabe wa mijinta da jam'iyyar. Yanzu ma ana neman gudummawarta. Duk abun da ta fada domin ta taimaki jam'iyya ne saboda akwai 'yan jam'iyya da suke gunaguni..
To saidai wai kalamun matar shugaban kasa tuni ya raba 'yan siyasar jihar ta Adamawa, jihar da ita Aisha Buhari ta fito.
'Yan'yan jam'iyyar PDP mai mulki suna murna da kalamunta. Onarebul Abdullahi Turem tsohon kwamishanan yada laabaran jihar kuma sakataren tsare-tsare na PDP din yace abun da suka sha fada ne ke faruwa. Sun yadda Buhari mutumin kirki ne amma wadanda suke kewaye dashi akwai muggayen mutane cikinsu. Su ma 'yan APC suna fadan hakan.
Su ma 'yan tsohuwar jam'iyyar CPC masu matukar goyon bayan Shugaba Buhari sun ce ya zama wajibi a akan Aisha Buhari ta fadi abun da ta fada , da bata yi ba da Allah ya tambayeta.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5