Yanzu dai gwamnatin ta tallata jiragen shugaban kasa guda biyu cikin guda goma sha daya.
Tun kuma faduwar farashin man fetur ake ta rade radin sayar dasu abun da can baya ba za'a taba tunanen hakan ba domin su ne kashin bayan tattalin arzikin kasar.
Mukaddashin bunkasa hanyar zuba jari da raba arzikin kasa Shettima Umar Abba Gana yace babu laifi idan aka sayar da kadarorin da basu samar da riba. Amma wadanda suke kawo riba bai makata a sayar dasu ba.
Yace akwai lokacin da aka sayar da kamfanin siminti da otel duk sun dace a yi hakan. Amma duk kamfunan da suke kawo riba bai kamata a sayar dasu ba.
Wani masanin tattalin arziki Abubakar Ali ya nuna fargaban cewa ko an sayar da kadarorin ba zasu taimaki farfado da tattalin arzikin kasar ba. Shi ma tsohon kwamishanan kudin jihar Gombe Inuwa Yahaya bai ga fa'idar sayar da kadarorin ba.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.