Jam’iyun hamayya takwas na kasar Liberia sun ce zasu janye daga zaben shugaban kasar da aka gudanar kwanan nan, bisa zargin cewa, an tafka magudi wajen kirga kuri’un, abinda suka ce ya sabawa damokaradiya.
A cikin sanarwar da suka bayar jiya asabar, jam’iyun sun ce jami’an zabe sun murde sakamakon zaben domin ba shugaba mai ci yanzu Ellen Johnson Sirleaf galaba, wadda bisa ga sakamakon zaben da aka sanar jiya jumma’a take kan gaba.
‘Yan takarar da ke barazanar janyewa sun hada da babban abokin hamayyar Mrs Sirleaf Winston Tubman, wanda ya zo na biyu, da kuma mai bi mashi a matsayi na uku, tsohon shugaban ‘yan tawaye Prince Johnson.
Hukumar zaben kasar Liberiya bata maida martani kai tsaye dangane da zargin magudin zaben ba. Tana kira ga dukan jam’iyun su bi matakan da doka ta shinfida wajen gabatar da korafinsu.
Ranar Jumma’a jami’an gudanar da zabe suka ce Madam Sirleaf tana kan gaba da sama da kashi 45% na kuri’in, yayinda Tubman yake da kashi 30% Johnson kuma ya sami kashi 11%.
Masu sa ido kan yadda aka gudanar da zaben na kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, sun bayyana zaben da aka gudanar ranar 11 ga wannan wata na Oktoba a matsayin mai sahihanci da cewa, ana kirga kuri’u lami lafiya. Cibiyar tsohon shugaban kasar Amurka Carter center ta bayyana samun kura kurai kalilan kawai.