Jam’iyun kawancen adawa na FRDDR a Jamhuriyar Nijar, sun gudanar da zanga zangar lumana a yau Lahadi a birnin Yamai.
Gamayyar jam’iyun ta ce ta gudanar da zanga zangar ce domin jan hankalin hukumomi akan abinda ta kira "mulkin kama karyar" da ya jefa ‘yan kasar cikin kuncin rayuwa.
Magoya bayan jam’iyun sun yi tattaki daga wani dandali a Birnin na Yamai zuwa wani yanki da ke kusa da majalisar dokokin kasar.
“Ka san wannan shekarar ba a tabuka komai ba, sai zalunci sai rashin karatu sai rashin magani a likita (asibiti).. ga yunwa.” Inji Kakakin jam’iyar RDR ta kawance FRDDR, Alhaji Dudu rahama.
Sai dai jam’iya mai mulki ta PNDS tarayya, ta ce duk matsalolin da ‘yan adawan suka zayyana ba su da tushe ballantana makama.
“In ka dauki maganar kiwon lafiya aikin da aka yi a wannan fanni, yau ‘yan kasa sun kare tafiya Morocco ko Algeria neman magani.” Inji Kakakin jam’iya mai mulki, Assoumana Muhammadou.
Saurari rahoton Sule Mumuni Barma domin jin karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5