Bayar da ilimi kauta ga yaro har zuwa shekaru goma sha shida, a duniya na daga cikin alkawuran da shugaban kasar Nijar Issoufu Muhammadou, yayi a yayin yaki neman zabe, domin a cewarsa fanin ilimi masamman ga ‘ya’ya mata wata mahimmiyar hanya ce ta samarda cigaban al’uma.
Sai dai shugaban kare hakkin yara ta APAD, Mousa Sadiku, nacewa wanna yunkuri na tafiyar Hawainiya. Yana mai cewa duniya a yau ta canza, babu wani cigaba da za a samu idan ba a dai daita hakkin maza da mata ba. Yace kananan mata a kasar Nijar, sun cikin matsala ta samun ingantacen ilimi.
Wata matsalar dake ciwa irin wadannan kungiyoyi tuwo a kwarya shine batun aurar da ‘yan matan da shekarunsu basu kai na aure ba, ya kara da cewa hada aure da karatu a matakin firamare ko kuma sakandare abune mai wuhalar gaske, amma aure da karatun jami’a wannan yana tafiya dai dai.
Hakama itama kungiyar kungiyar WILFAD, a nata bangare tana cigaba da yin gargadi akan wannan alamari dake bukatar samun hadin kan iyaye da suma matasan da kansu.
Bayanai na nuni da cewa fiye da rabin alumar Nijar Mata ne, yayinda aka gano cewa kusan kashi saba’in na jama’ar kasar Nijar duk matasa nelamarin dake nuna jinsin mata mafi fama da matsalar rashin samun ilimi, kuma a baya bayan nan shugaban kasar Nijar, yace mazauna karkara ne suka fi fama da talauci a kasar ta Nijar.
Facebook Forum