Shugaban hukumar Civil Defense a jihar Nasarawa Muhammad Gidado Fari, ya ce sun sami nasarar ne biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu daga jami’ansu.
Jami’an sun kama mutane biyu dauke da bindigogi, haka kuma sun kama wasu ‘yan fashi guda biyu da kuma wani da laifin lalata dukiyar gwamnati. Shugaban hukumar yace baki ‘daya wadanda aka Kaman za a gurfanar da su gaban kotu.
Wasu daga cikin wadanda aka Kaman sun yiwa Muryar Amurka bayanin laifukan da aka kamasu da yi.
Daga can yankin da ake rikici tsakanin kabilar Basa da Ibra a karamar hukumar Toto, mai magana da yawun ‘yan kabilar ta Bassa Usman Gimba, ya ce babbar bukatarsu itace su sami masarauta da zata dakile duk wani rikici tun kafin ya kai ga rasa rayuka da dukiyoyi.
Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tanko Almakura ya yi alkawarin ziyartar yankin don samun hanyar shawo kan rikicin.
Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5