Jami’an tsaron da suke biyaya ga shugaba Laurent Gbagbo sun bude wuta akan taron magoya bayan shugaban masu hamaiya Alassane Ouattara

UN peacekeepers drive past supporters of Alassane Ouattara as they demonstrate and burn tires in the Abobo neighbourhood in Abidjan.

Shedun gani da ido a kasar Ivory Coast sunce jami’an tsaron da suke biyaya ga shugaba Laurent Gbagbo sun bude wuta akan taron magoya bayan shugaban masu hamaiya Alassane Ouattara harma suka kasha akalla mutum biyu

Shedun gani da ido a kasar Ivory Coast sunce jami’an tsaron da suke biyaya ga shugaba Laurent Gbagbo sun bude wuta akan taron magoya bayan shugaban masu hamaiya Alassane Ouattara harma suka kasha akalla mutum biyu. Shedun gani da ido sunce jami’an tsaro sunyi harbi kuma suka harba barkonon tsohuwa akan daruruwan mutane yawancinsu matasa magoya bayan Alassane Ouattara a wasu unguwani guda biyu na birnin Abidja. Kasashen duniya da dama sunce Lassane Ouattara shine ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a watan nuwamban bara. To amma shugaba Gbagbo yaki yayi na’am da bukatun kasa da kasa cewa ya sauka daga kan ragamar mulki, matakin daya zama sanadin samun rikicin siyasa dana tattalin arziki a kasar. A yau lahadi aka shirya kwamitin kungiyar kasashen Afrika zai yi wani taro a kasar Mauritania domin tattauna hanyoyin magance rikicin Ivory Coast. Kwamitin ya kunshi shugaban kasar Burkina Faso da Chadi da Mauritania da Afrika ta kudu da kuma Tanzania. An shirya shugabanin kasashen guda biyar gobe litinin zasu je Ivory Coast domin ganawa da Mr. Gbagbo da Mr Ouattara.