Jami'an Tsaro na Tsananta Binciken Motoci a Nyanya

Harin bom a Nyanya, kilomita 16 daga tsakiyar birnin Abuja, Afrilu 14, 2014.

Bayan fashewar bama-bamai a Nyanya kusa da Abuja da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma raunata wasu da yawa, jami'an tsaron Najeriya sun tsananta tsaro da biniken kwakwaf na ababen hawa
Fashewar bamabamai da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma jikata wasu ya sa jamai'an tsaro sun fantsama koina a Abuja da kewaye suna binciken ababen hawa.

Babu abun mamaki yadda jami'an tsaro suka shiga binciken kwakwaf na ababen hawa dama jama'a dake tafiya. Matakan tsaron sun fi shafar ma'aikata dake sammako zuwa aiki cikin garin Abuja kana kuma da yamma su yi jerin gwano komawa 'yan garuruwan dake kewaye da birnin na Abuja.

Lokacin da shugaba Jonathan ya ziyarci inda lamarin ya faru ya jajantawa wadanda aika aikar ta rutsa da su, wadanda basu san hawa ba balantane sauka. Jonathan ya dora alhakin harin kan kungiyar Boko Haram wadda yace gwamnatinsa zata maganceta.

Kawo yanzu babu wata sanarwa da ka iya dora alhakin harin kan kungiyar ta Boko Haram. Saidai jam'iyyar PDP ta fitar da sanarwa inda ta alakanta aukuwar harinda kalamun da tace 'yan adawa na APC keyi dake ingiza kashe rayuka da asarar dukiya. Sakataren jam'iyyar ya dora alhakin tashe tashen hankalin kan jam'iyyar APC wadda yace ta lashi takobin hana Jonathan mulki ganin yadda talakawa suka amince da milkinsa.

Tuni APC tayi watsi da zargin na PDP. Keften Bala Jibrin dan kwamitin zartaswar jam'iyyar APC na kasa yace mutanen PDP sun gagara yin mulki domin sun kasa amma kuma suna son su dorawa wani laifi wanda bai san hawa ba bai san sauka ba. Yace su ne suke rike da duk jami'an tsaron kasar. Yace idan ba zasu iya ba, ba abun kunya ba ne Jonathan yayi murabus gobe yace ya bar aikin a ba wadanda zasu iya.

Alkaluman 'yan sanda na nuna cewa mutane 71 da daya suka mutu kana fiye da dari suka samu raunuka. Saidai alkaluman da ba na hukuma ba na cewa wadanda suka rasu sun kai dari biyu.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Jami'an Tsaro Sun Tsananta Binciken Motoci Bayan Fashewar Bamabamai a Nyanya - 2'16"