ZABEN2015: Jami'an Tsaro Sun Shiryawa Zabe a Jahar Adamawa

'Yan Sandan Najeriya

Jihar Adamawa na daya daga Jihohin Najeriya da ake saka wa idanu don fargabar kar zaben wajen ya zo da tangarda, musamman ma idan aka yi la'akari da yada lamuran tsaro ke tafiya a yankin na Arewa maso Gabashin kasar. Wannan ce tasa aka yi shiri na musamman don gujewa matsala.

A wata hirar da wakilin muryar Amurka yayi da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa Usmanu Abubakar a dangane da tanadin da suka yiwa jihar akan harkar tsaro a lokacin babban zaben kasa da za'a yi ranar 28 ga wannan wata na Maris ganin sun yi wani taron hadin gwiwar da jami'an tsaro.

Usmanu yace, "Duk ma'aikatanmu da ya kamata su yi wannan aiki kamar su jami'an hana fasa kwauri, jami'an tsaron na fari kaya, jami'an Shige da Fice dana 'yan sanda suna shirye kuma yanzu haka kowa ya riga ya san wurin aikinsa".

Jami'in 'yan sandan ya yi kira ga daukacin jama'ar Adamawa da su kwantar da hankulansu kuma su yi zaben cikin kwanciyar hankali da lumana. Yace rundunar 'yan sanda ta riga ta shirya kuma zata bada kariya a wajen wannan zabe har ma da bayan zaben.

Itama hukumar zaben Najeriyar INEC tace, tana kan gudanar da shirye-shirye domin gudanar da wannan zabe kamar yadda wakilin na muryar Amurka yayi hira da kwamishinan zaben jihar Adamawan Alhaji Baba Abba Yusuf. Ya bayyana cewar sun kammala kai kayayyaki kananan hukumomi, kuma sun wayar da kan jama'a. Dan haka babu abin da ya rage sai dai jiran lokacin kada kuri'u kawai.

A bangaren talakawa kuma, yawancin jama'a sun nuna a shirye suke domin fitowa kwan su da kwarkwatar su domin kada wannan zabe a jahar Adamawa kuma wasu sunyi karin bayanin cewa basu da wani fargaba ko tsoron fita wajan wannan zabe.

Sai dai kuma wasu daga cikin yankunan Madagali da Michika da aka kwato daga hannun kungiyar boko haram, suna kira ne da a maida su garuruwansu domin su kada kuri'unsu.

Daga karshe kakakin majalisar jihar wanda shima dan yankin Madagalin ne Honurable Ahmad Amadu Fintiri yace yunkurin kai 'yan gudun hijira wuraren yin zaben da ake fadi ba da yawun su bane.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN 2015: Jami'an tsaro sun yi shirin zabe a Adamawa - 3'25"