Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe Sojoji Bakwai


Wurin da bam ya tarwatsa a Libya
Wurin da bam ya tarwatsa a Libya

Wani dan kunar bakin wake ya kashe sojoji bakwai a Benghazi dake kasar Libya

Wani dan kunar bakin wake ya kutsa da motarsa cikin sojojin dake duba ababen hawa a Birnin Benghazi kasar Libya.

Ya kashe akalla sojoji bakwai

Wani rahoto yace mutane biyu ne ke cikin motar.

Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin to amma ana kyautata zato mayakan sa kai ne masu kishin Islama suka kai harin.

Dama mayakan Islaman sun kwace babban Birnin kasar inda suka kafa tasu gwamnatin suka kuma tilastawa gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita ficewa zuwa gabashin kasar.

Harin na jiya Talata yazo ne daidai lokacin da wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman akan Libya, Berardino Leon ya kawo shawarar kafa gwamnatn hadin gwiwa a kasar.

Shawarar tashi wani kokari ne na kawo karshen abun da ya kira dagulewar yaki.

Tashin hankali da rikicin siyasa sun addabi kasar ta Libya tunda aka hambare aka kuma ksashe shugaba Moammar Gadahafi a shekarar 2011, mutumin da ya kwashi shekaru da dama yana yiwa kasar mulkin kama karya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG