Jami’an Tsaro Sun Budewa Masu Zanga Zangar Neman Hakkinsu Wuta A Jihar Adamawa

Masu aikin sarar Rake na kamfanin sarrafa sukari na Savannah, mallakar gamayyar kamfanonin Dangote guda biyar da ake yi wa jinyar raunukan harbin bindiga a babban asibitin garin Numan, da ke jihar Adamawa, bayan wata zanga-zanga da ta barke ranar Litinin da yamma sakamakon kin amincewar ma’aikatan na jinkirta biyansu hakinsu na wata guda.

Ma’aikatan wadanda ke aikin kwadago na ci da guminka, sun fusata ne lokacin da aka kira su harabar bankin Banghe inda suka yi zaman jira har na tsawon sa’o’i Bakwai amma daga baya aka ki biyansu.

Shaidun gani da ido irinsu Mallam Memu Sama’ila da Sunday Mijah sun ce sun ji karar harbe-harben bindiga lokacin da jami’an tsaro suka nemi tarwasa su, lamarin da ya yi sanadiyyar jikkata wasu.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar ma’aikatan da ya nemi in sakaya sunan sa da kuma jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan Sandan jihar Adamawa ASP Othman Abubakar, sun tabbatar da afkuwar lamarin. Sai dai shugabannin kanfanin sarrafa Sukari na savannah mallakar kanfanonin Dangote da na bankin Banghe wanda ta hanunta ake biyan ma’aikatan sun ki cewa komai har sai sun sami umurni daga magabatan su.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Jami’an Tsaro Sun Budewa Masu Zanga Zangar Neman Hakkinsu Wuta A Jihar Adamawa - 3'26"