Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Hadin Gwiwa Tsakanin Afirka Ta Kudu Da Najeriya Wajen Yakar Ta’addanci


Sojojin Najeriya sun ceto wasu mutane a bayan da suka fatattaki 'yan Boko Haram daga wani sansaninsu dake dajin Sambisa a Jihar Borno
Sojojin Najeriya sun ceto wasu mutane a bayan da suka fatattaki 'yan Boko Haram daga wani sansaninsu dake dajin Sambisa a Jihar Borno

A wani taron ganawa da akayi tsakanin ministan tsaron Afrika ta Kudu da jami’an ma’aikatar tsaron Najeriya, gabannin ziyarar da shugaba Jacob Zuma zai kai birnin Abuja a yau Talata.

Mrs. Nosiviwe Nqakula, ministan tsaron Afirka ta Kudu, tace a wani lokaci cikin shekarar nan zamu yi taro na musammam tsakanin ma’aikatan kasashen biyu Najeriya da Afirka ta Kudu, inda za a yi musayar dabarun yaki da ta’addanci.

Ministan tsaron ta kara bayyana wasu sassa da suka hada da nuna dabarun kariyar sararin samaniya da Afirka ta Kudu zata gayyaci Najeriya, wanda za ayi a birnin Johannesburg a watan Satumba. Wannan dai hadin kan kasashen Afirka biyu masu tasiri na da muhimmanci a yunkurin kungiyar Afirka AU wajen yaki da ta’addanci.

Shima ministan tsaron Najeriya, Mansur Dan Ali, yace “muna duba yadda kasashen namu guda biyu zasu hadu da sauran manyna hafsoshin soja domin a fito da wata manufa da kasashen biyu zasu amfana…” inda ya ci gaba da bayyana yadda yaje kasar Afirka ta Kudu, ya gano kayayyakin aikin da Najeriya take bukata, har ma su taimakawa Najeriyar wajen kera makamai da ake a jihar Kaduna.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG