Duk da kiraye-kirayen da Janaral Buhari dan takarar mukamin shugaban kasa yayi da sauran 'yan siyasa cewa gwamnatin tarayya ta dauki mataki akan bijirarrun nan na Niger Delta har yanzu shiru a keji kamar an shuka dusa.
Su 'yan tsageran Niger Deta sun yi taro ne a gidan gwamnatin Bayelsa inda suka yi barazanar tada zaune tsaye idan har ba'a zabi Shugaba Jonathan ba a zaben watan gobe. Duk da barazanar da suka yi babu wani abu da mahukuntan kasar suka yi ko suka ce.
Sani Aminu Dutsenma wanda ya nemi jam'iyyar PDP ta tsayar dashi dan takarar shugaban kasa a shekara ta 2011 tare da Goodluck Jonathan ya fito fili yayi alawadai da kalamun 'yan Niger Delta din da kuma yadda jami'an tsaro suka tsuke bakinsu.
Yace maganganun da 'yan tsagerun Niger Delta suka yi can baya ba'a daukesu da wani mahimmanci ba domin ana ganinsu kaman na gidan jiya ne. Amma maganar da suka yi ranar Juma'a magana ce mai karfi domin an yita ne a gidan gwamnatin Bayelsa. Gwamnan Bayelsa ya kasance a wurin. Mataimakinsa na wurin. Bugu da kari mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin Niger Delta Kingsley Kuku yana wurin. Akwai kuma wasu makarraban gwamnati.
'Yan Niger Delta din sun ce su ashirye suke su yaki Najeriya idan ba'a zabi Jonathan ba. Wai kuma rashin zabansa kalubala ne ga kabilar Ijaw. Abun tsoro ne a ce jami'an gwamnati suna zaune aka yi maganar kuma tun ranar Juma'a da suka yi maganar kawo yanzu babu abun da aka yi a hukumance.
Sani yace ba 'yanci ba ne mutum ya fito yace zai yaki kasa idan ba'a zabi wani mutum ba. Inji Sani ya kamata a kula da wani abu. Tompolo shugaban 'yan tsageran shi ne gwamnati ta baiwa tsaron hanyoyin ruwan kasa. Kwana kwanan nan Tompolo ya je Norway ya sayo jiragen yaki na ruwa guda bakwai. Ban da haka ana zargin cewa jirgin shugaban CAN Orisajeafor da ya tafi Afirka Ta Kudu sayen kayan yaki da Asari Dokubo cikI.
Akwai abun lura a lamarin.
Ga cikakken bayani.
Your browser doesn’t support HTML5