Jami'an Tsaro Basu Taka Doka Ba

Gawarwakin matasan da aka kashe

Majalisar Dattawan Najeriya ta ce samamen da jam'an tsaro suka kai wani gida a Abuja inda suka kasha matasa takwas bai saba ma doka ba
'Yan watannin da suka wuce kasar Najeriya ta tashi taji cewa jami'an tsaro sun kashe wasu 'yan kungiyar Boko Haram dake boyewa a wani gida da ba'a gama ginawa ba a anguwar Apo cikin Abuja.

Kisan da jami'an tsaro suka yi ya kawo shakku a zukatan mutane yayin da aka gane 'yawancin wadanda ke cikin gidan 'yan kungiyar keke napep ne. Sabili da cecekucen da ya taso majalisun dokokin Najeriya suka kaddamar da bincike.

Jiya majalisar dattawa ta sanarda matsayinta kan rahoton kwamitin da ta nada karkashin Janaral Muhammed Magoro mai ritaya. Majalisar ta ce samamen da jami'an tsaro suka kai gidan da ya yi sanadiyar mutuwar wasu matsa bai taka doka ba sai dai an kaishi cikin gaggawa. Kamata ya yi da jami'an sun kara bincciken rahoton da suka samu.

Sai dai matsayin majalisar dattawan bai yiwa kungiyar keke napep dadi ba. Dalili ke nan suka garzaya ofishin Muryar Amurka inda suka bayyana rashin amincewarsu da matsayin majalisar da kuma bacin ransu. Shugaban kungiyar Musa Ibrahim ya ce basu gamsu da rahoton ba ko kuma matsayin majalisar. Abun ya zo masu ba zata ya kuma bata masu rai. Ya ce dama dalilin jinkirta rahoton domin mutane su manta da abun da ya faru ne! Y a ce rahoton karya ya fada ba gaskiya ba ne. Idan an ce wasu suna boye domin su kai hari a Abuja ya nuna ke nan jami'an tsaro ko basu san abun da suke yi ba ko kuma basa yin aikinsu yadda ya kamata. A cikin gari kamar Abuja jami'an tsaro basu san yadda zasu tabbatar da tsaron birnin ba?

Musa Ibrahim ya ce suna da zabi uku. Zasu rubuta wasikar korafi kan jamai'an tsaro abu na daya ke nan. Suna shirin su garzaya kotu, matakin da suka jinkirta domin an basu tabbaci cewa gwamnati zata yi wani abu. Abu na karshe zasu yi gangami a Abuja na nuna kin amincewarsu da majalisar dattawa da kuma jawo hankalin gwamnati ta aiwatar da gaskiya.

Mai magana da yawun SSS Merylin Ogah ta ce hakin hukumar ne ta tsare lafiyar 'yan Najeriya da dukiyoyinsu. Shi kuwa Umar Garkuwa wani mazaunin Abuja ya ce duk abun da aka kai majalisar dattawa ba za'a yi masa adalci ba. Ya ce wani hali ne suka samu kansu bisa ga kuskuren da suka yi. Yau idan an kashe Hausa da Fulani babu abun da zai faru. Amma Malam Musa Suleiman Mohammed ya ce wanda ya shuganci kwamitin tsohon janaral din soja ne. Ya san harkar tsaro. Abunda jami'an tsaro suka gabatar ma kwamitin shi suka yi aiaki da shi. Don haka yana goyon bayan rahoton.

Ga Medina Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Jami'an Tsaro Basu Taka Doka Ba - 3:44