Jami’an kasar Masar sunce sun bude wuta akan wasu ‘yan yawon bude ido da suka yi zaton ‘yan kungiyar ta’addanci ne wadanda suka ratsa ta wani kebabben waje su kuma jami’an tsaro suka bude musu wuta suka kashe akalla mutane 12 ciki har da ‘yan kasar Mexico 2.
Ma’aikatar harkokin wajen Masar tace, sojoji da ‘yan sandan na fakon ‘yan ta’adda ne da ke amfani da motocin da suke kira four-by-four, kwatankacin irin wadanda ‘yan yawon shakatawar suke ciki ranar Lahadi a Farafra da ke yankin hamada ta Masar din.
Mutane 6 da suka tsira sun gayawa jakadan kasar dake Masar cewa an yi musu luguden wuta da jiragen yaki da jirage masu saukar Ungulu. Shugaban kasar Mexico Enrique Pena Nieto ya bukaci a gudanar da bincike akan lamarin da har ‘yan kasar Misiran ma da dama suka halaka.
Shugaban yace Mexico ta yi Allah wadai da wannan garajen kisan kan 'yan kasar,daga nan ta bukaci a gudanar bincike mai tsanani kan abunda ya auku". Kamar yadda ya fada a shafinsa na twitter ranar lahadi.
Kakakin ma’aikatar yawon bude ido ta Masar Rasha Azazi ya yi magana da yawun hukumarsu.
Yace, kamfanin da yayi kamashon ‘yan yawon bude idon, bashi da cikakken izinin zuwa wajen, sannan basu sanar da hukumomi cewa za su kai ‘yan yawon shakatawar zuwa wajen ba, kasancewar sai an sanar da hukumomi idan za'a je Farafra. Kamar yadda ya fadawa kamfanin dillancin labaran AP.