Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EGYPT: Shin Hukuncin da Aka Yiwa Wasu 'Yan Jarida Nada Nasaba da Siyasa


Shugaban Masar Abdel-Fattah el-Sissi,
Shugaban Masar Abdel-Fattah el-Sissi,

Wani danjaridan kasar Australia mai suna Peter Greste ya fada jiya Lahadi cewar, hukuncin da aka yanke masa da abokan aikin sa biyu shekaranjiya Assabar a kasar Masar na da nasaba da siyasa

Yanzu shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sissi nada damar “gyara wannan rashin adalcin”, wajen sakin ‘yan jaridun uku.

Wata kotun Masar ce dai ta samu ‘yan Jaridar uku: Greste da Mohammed Fahny ‘dan asalin Canada da Baher Mohammed ‘dan Masar, da laifin goyon bayan haramtacciyar kungiyar nan ta Muslim Brotherhood da yanke musu hukuncin ‘daurin shekaru uku a gidan yari.

Greste dai ya koma Autralia a farkon shekarar nan, yayinda su kuma Mohammed da Fahny aka sake su ne kan baili, kafin ‘daukar su zuwa kurkuku ranar Asabar din data wuce.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta nuna matukar damuwar ta kan wannan hukunci da aka yanke, ta kuma yi kira ga Masar da tayi duk abinda ya dace domin tabbatar da an gyara lamarin. Mai magana da yawun ma’aikatar, John Kirby yace, ‘yancin ‘yan jarida ginshiki ne ga ci gaban dimokaradiyya a kowace kasa ta duniya.”

XS
SM
MD
LG