Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EGYPT: Masar ta Ayyana Dokar Yaki da Ta'adanci


'Yansandan 29 da 'yan ta'ada suka kashe a Masar
'Yansandan 29 da 'yan ta'ada suka kashe a Masar

Shugaban Masar Abdul Fatah al Sisi, ya saka hanu kan wata dokar yaki da ayyukan ta’addanci, wacce ta tanadi hukuncin kisa da na daurin rai-da-rai ga duk wanda aka samu da hanu a ayyukan ta’addanci.

Dokar har ila yau ta tanadi cin tarar duk wani dan jarida da aka samu ya yada labaran da ba daidai ba.

A watan Yunin da ya gabata Mr Sisi ya yi alkawarin karfafa dokar yaki da ta’addanci, bayan da wani harin bam ya kashe babban mai shigar da kara a kasar.

Shugaban dai ya dora alhakin kisan akan kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta Muslim Brotehrhood, kungiyar da gwamnatinsa ta yiwa shaidar cewa ta ‘yan tadda ce, wacce kuma ya ke ta kassarawa, tun bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Mohammed Morsi a watan Yulin 2013.

A karkashin dokar, duk wanda aka samu da laifin jagoranta ko kuma kafa wata kungiyar ‘yan ta’adda, zai fuskanci hukuncin kisa, kana samar da kudade ga kungiyar zai janyowa mutum hukuncin daurin rai-da-rai, yayin da tunzura mutane domin su gudanar da ayyukan ta’addanci shima aka tanadi hukuncin zaman gidan yari.

Ga ‘yan jarida da suka ba da rahoton da ya sabawa, wanda hukumomi suka fitar, za su fuskanci cin tara ta Dala dubu 25 zuwa 64.

XS
SM
MD
LG