Jami'an Kiwon Lafiya Daga Najeriya Da Wasu Kasashe Sun Yi Taro A Nan Amurka

jami'in kiwon lafiya yana cire tsutsar kurkunu daga kafar wani yaro a kasar Ghana

Ajandar taron bana ita ce yadda za a kulla a kuma cin moriyar kawance a tsakanin cibiyoyin lafiya da kamfanonin sarrafa magunguna domin takalar matsalolin dake addabar harkar kiwon lafiya a kasashen na Afirka

A wurin taronta na shekara-shekara na hudu da ta yi kwanakin baya kan Bunkasa Kiwon lafiya a Afirka, kungiyar "Global Health Progress" ta gudanar da tarurrukan mako guda da jami'an kiwon lafiya tare da masu hannu a harkokin kiwon lafiya daga kasashen bakar fata 7 na nahiyar Afirka.

An gudanar da wadannan tarurruka a biranen Washington DC da kuma New York.

Kungiyar "Global Health Project" ko GHP a takaice, gamayya ce ta kamfanonin harhada magunguna wadanda suka damu da irin nauyin cututtukan dake addabar nahiyar Afirka fiye da kowace nahiya. Kungiyar tana zaman dandalin musanyar sabbin ra'ayoyi da dabarun yaki da cuce-cuce a nahiyar Afirka.

Wakilan da suka halarci tarurrukan wannan shekara sun hada da jami'an kiwon lafiya daga Najeriya da Ghana. Sauran sun hada da na kasashen Botswana, Kenya, Lesotho, Swaziland da kuma Uganda. Tarurrukan na bana sun samu halarci fiye da kowane lokaci a can baya.

Bisa la'akari da taken tarurrukan na bana, watau Bunkasa Hanyoyin Samun Ci Gaba ta Hanyar Karfafa Kawance, wakilai sun tattauna yadda kulla kawance a tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin lafiya ta taimakawa kasashensu wajen shawo kan wasu cututtukan. Sun kuma yi aiki tare da dukkan wakilai na taro domin gano sauran matsalolin da suka rage da yadda za a iya kulla kawance domin shawo kansu nan gaba.

A duk tsawon mako gudan da aka yi ana wadannan tarurruka, wakilai sun bayyana abubuwan da suka fuskanta, da ra'ayoyinsu da kuma kwarewarsu kan yadda za a shawo kan cututtukan tare da jami'an gwamnatin shugaba Barack Obama, da wakilan majalisar dokokin Amurka, da na sassa masu zaman kansu, da kungiyoyin agaji, da gidauniyoyi da kuma jami'o'i.

Haka kuma sun yi bukukuwan murnar cewa a bana Amurka zata fadada ayyukan kiwon lafiyar da take tallafawa a kasashen duniya.