Babban Bankin Duniya yayi gargadi game da tashin gwauron zabin farashin kayan abinci, da kuma bukatar dake akwai ga manyan kasashen dun iya masu hannu da shuni da su maida hankali kan yadda za a iya samar da wadataccen abinci.
Alkaluman Farashin Abinci na Bankin Duniya sun nuna cewa an samu karuwar kashi 29 cikin 100 a farashin kayan abinci idan an kwatanta da wannan lokaci a shekarar da ta shige. Haka kuma wannan adadin, yayi kusan kaiwa ga mummunan tashin farashin da aka gani na watan Yunin 2008. Wannan kuwa, babban abin damuwa ne.
Babban abinda ya haddasa cirawa saman da alkaluman suka yi shi ne mummunan tashin farashin alkama, da masara, da sikari da kuma man girki. Babban abin farin cikin da ake gani in ji bankin, shi ne farashin shinkafa a kasuwannin duniya bai tashi kamar yadda na alkama da wasunsu yayi ba.
Amfanin gona mai yawa da albarka da aka samu a bara a kasashen Afirka da dama, ya sa ba a ga mummunan tashin farashin kayan abinci a bana ba a kasashen. Amma akwai kasashen Afirka da dama inda wannan abu yayi muni, kamar kasar Burundi inda farashin wake ya tashi da kimanin kashi 48 cikin 100. Wake na daya daga cikin muhimman kayayyakin abinci a Burundi.
A yanzu dai farashin kayayyakin abinci a kasuwannin duniya sun kai mizani mai hatsari. Ya bayyana a fili cewa tashin farashin da aka gani cikin 'yan kwanakin nan ya jefa talakawa a fadin duniya cikin karin wahala.
Bankin Duniya yayi hasashen cewa karin farashin na 'yan kwanakin nan ya jefa mutane kimanin miliyan 44 cikin bakin talauci. Tun ma kafin wannan karin farashin, akwai mutane fiye da miliyan 900 dake kwana da yunwa kowace rana a duniya.
Shugaban Bankin Duniya, Robert B. Zoellick, yace ana bukatar duniya ta kara zage damtse domin tabbatar da cewa an ciyar da masu kwana da yunwa, da kuma fuskantar kalubalen ciyar da mutane miliyan dubu tara da ake jin za a samu a duniya nan da shekara ta 2050.
Ana iya kallon cikakken bayanin da shugaban bankin na duniya yayi kan yakar yunwa da wadatar da duniya da abinci ta hanyar Youtube ta hanyar matsa wannan mahada dake kasa.