Jami'oin Gwamnatin Nijer Sun Shiga Yajin Aikin Kwanaki Uku

A yau Talata ne malaman jami’oin gwamnati suka fara yajin aikin kwanaki 3 a jamhuriya Nijer, da nufin tilastawa hukumomi daukar matakan magance wasu matsalolin da suka shafi yanayin rayuwa da aiki, sai dai ministan ilimi mai zurfi na mamakin matakin na kungiyar malaman jami’a.

Kin cika wasu daga cikin alkawurran da gwamnati ta dauka yayin wata tattaunawa da aka yi kwanakin baya tsakanin shugabannin kungiyar malaman da gwamnati yasa malamai dakatar da ayyukan koyarwa daga yau Talata zuwa Alhamis a daukacin jami’oin gwamnatin kasar.

Maga takardar kungiyar malaman jami’oin gwamnatin jamhuriyar Nijer, Malam Sahabi Bakaso, ya bayyana cewa ranar jumma’ar data gabata sun tattauna da ministan ilimin kasar amma tattaunawar bata gamshi ‘ya’yan kungiyar malaman ba.

Malam Sahabi, ya ce kawo yanzu wasu da dama daga cikin malaman jami’oin basu sami albashinsu na watan da ya gabata ba, har ma da sauran wasu alawus-alawus da ya kamata gwamnati ta biya amma babu labari.

Sai dai kuma ministan ilimin kasar Malam Yahuza Salisu, na kallon lamarin a matsayin wani abin bazata, domin a cewar sa, tilas ne gwamnati zata kammala biyan malaman albashinsu kana daga bisani ta biya alawus din da suka rage.

Tuni dai lamarin ya fara tada hankalin dalibai saboda yadda tasirinsa ka iya shafar jaddawalin karatun wannan shekarar a cewar daliban. Wannan shine karo na biyu da kungiyar malaman ke tsunduma cikin yajin aiki daga watan satumbar shekarar data gabata.

Wakilin muryar Amurka a Yamai Sule Mumuni Barma ya aiko mana Karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Jami'oin Gwamnatin Nijer Sun Shiga Yajin Aikin Kwanaki Uku