A makon gobe ne ake sa ran shugaban Amurka Donald Trump zai ayyana yarjejeniyar Nuclear da Amurka da wasu manyan kasashen duniya suka kulla da Iran a zaman gurguwar yarjejeniya, da kiris yake rage shugaban ya ayyana yarjejenbiyar a zaman maras tasiri.
Shugaba Trump zai fada cewa yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 2015, ba zata taimaki tsaron Amurka.
Matakin zai kaddamar wa'adin kwanaki 60 ga majalisun dokokin AMurka su yanke shawara ko zasu sake kakakabawa Iran takunkumin karya tattalin arziki,da aka janye bayan da aka cimma yarjejeniyar.
Wakilai 'yan jam'iyyar Democrat da Republican masu yawa suna adawa da sake kakabawa Iran takunkumi, wanda yain hakan zai soke yarjejeniyar baki daya.
Ministan tsaron Amurka James Mattis da kuma babban hafsan hafsoshin Amurka Joseph Dunford duk sun gayawa majalisar dokoki cewa ci gaba da aiki da yarjejeniyar yana da tasiri ga tsaron Amurka.
Shugaban Iran Hassan Rouhani yayi barzanar Iran zata yi da yarjejeniyar da zarar Amurka ta sake aza mata takunkumi.
Facebook Forum