Jami'in Hukumar Kwastam Ya Mutu Yayin Ganawa A Majalisar Wakilai

Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)

Sanarwar da mai magana da yawun majalisar kuma shugaban kwamitinta akan harkokin yada labarai da hulda da jama'a, Akin Rotimi, ya fitar a yau Talata tace, yayin ganawar da misalin karfe 1 na rana, rashin lafiya ta rufe jami'in.

An tabbatar da mutuwar wani jami'in hukumar yaki da fasakwaurin Najeriya a yayin da yake halartar wata ganawa da kwamitin Majalisar Wakilai.

Sanarwar da mai magana da yawun majalisar kuma shugaban kwamitinta akan harkokin yada labarai da hulda da jama'a, Akin Rotimi, ya fitar a yau Talata tace, yayin ganawar da misalin karfe 1 na rana, rashin lafiya ta rufe jami'in.

An ruwaito Rotimi yana cewar, "a cikin alhini da takaici nake tabbatar da mutuwar jami'in hukumar kwastam dake ganawa da kwamitin majalisar."

Saidai majalisar, bata bayyana bayanan jami'in ba "a matsayin mutuntawa ga iyalansa".