Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Gangamin Da Sunday Igboho Ya Shirya A Legas

Yadda 'yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa kwalla wajen tarwatsa masu zanga-zanga a Legas

Rahotanni sun ce Sunday Igboho da jami'an tsaro ke nema ruwa a jallo, bai halarci gangamin ba.

Masu gangamin neman kafa kasar Yarbawa sun yi dandazo a dandalin Gani Fawehinmi da ke unguwar Ojota a jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya.

Sai dai rahotanni sun ce jami’an tsaro da aka girke tun da sanyin safiyar ranar Asabar sun tarwatsa masu zanga-zangar ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwan zafi.

Wata matashiya ta rasa ranta bayan da harsashin ‘yan sanda da aka harba ya kauce hanya ya same ta yayin da take zaune a shago kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Babu wani bayani daga hukumomin tsaro dangane da mutuwar matashiyar ko jikkatar wani a zanga-zangar.

A ranar Alhamis, rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta gargadi wadanda suka shirya gangamin da su janye gudun kada bata gari su yi amfani da shi wajen haifar da rudani.

Sunday Igboho, wanda ke jagorantar fafutukar ballewar yankin Yarbawa ne ya shirya wannan gangami.

Amma daga baya ya janye, bayan da hukumar tsaro ta DSS ta kai samame gidansa da ke birnin Ibadan a jihar Oyo.

Sai dai daga baya ya sake yakewar cewa a fita a yi gangami, ko da yake, rahotanni sun ce ba a ga Igbohon a wajen taron ba.

Kungiyar Ilano Omo O’dua da ke jagorantar gangami, ta yi ikirarin cewa zanga-zangar ta lumana ce.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito masu gangamin suna cewa, lokaci ya yi da za a kafa kasar Yarbawa, saboda babu alama zamansu a Najeriya zai kai su ga gaci.

Jama’a da dama sun rufe shagunansu a yankin Ojota da ke birnin na Eko saboda gudun barkewar mummunan rikici.

A ranar Alhamis hukumar ta DSS ta ayyana cewa tana neman Igboho ruwa a jallo, wanda asalin sunansa Sunday Adeniyi Adeyemo.

Hukumar ta DSS ta gano wasu makamai a gidan Igboho yayin samamen da ta kai wanda ya yi sanadin mutuwar wasu masu gadinsa biyu ya kuma jikkata jami’in tsaro daya.

Jami’an tsaron Najeriya sun ce masu gadin Igboho ne suka fara bude masu wuta a lokacin da suka isa gidan.