A yayin da mambobin kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’i ta SSANU, da na ma’aikatan jami’o’i da ba malamai ba ta NASU da JAC su ka fito zanga zangar lumana a dandalin Unity Fountain daga misalin karfe 7 na sanyin safiyar yau wanda ya yi daidai da ranar da gwamnatin tarayya za ta gana da kungiyar kwadago ta NLC don cimma matsaya akan mafi karancin albashi.
Jami’an tsaro musamman ma ‘yan sanda da DSS suka tare kofar shiga dandalin na Unity Fountain suka hana mambobin kungiyoyin fita su yi tattaki zuwa ofishin Ministan Ilimi don mika kökensu na rashin biyan hakokkinsu.
Lamarin dai ya kusa rikidewa zuwa ga tarzoma ganin yadda kwamishinan ‘yan sandan birnin Abuja, Bennett Igwe, ya zo da kansa tare da motoci sama da 5 ciki da motar yaki kirar gun truck a turance yana mai cewa ba mai fita yin zanga-zanga a kan titin Abuja daga cikin dandalin na Unity Fountain.
Kwamared Ikeguru Chukwugozie, shugaban kungiyar NAS , reshen jami’ar Nnamdi Azikiwe dake Awka, fadar gwamnatin jihar Anambra wato dake kudu maso gabas ya ce sun fito ne don mika kokensu ga yadda aka rike mu su albashi tun bayan yajin aikin da suka gudanar a shekarar 2022, ya na mai cewa sakon su abu ne mai sauki da gwamnati ta sani kuma yi musu barazana da bindigogi da wukake ya sabawa ka’ida a tsarin mulkin dimokradiyya.
A yayin zanga-zangar lumana da kungiyoyin suka shirya, ba’a bar yankin arewa maso gabas a baya ba inda wakilai daga jami’o’in gwamnatin tarayya daga Gombe, Bauchi da Adamawa..
Yankin arewa maso tsakiya ma ya sami wakilci daga jihar Kogi, inda sakataren SSANU a jami’ar gwamnati na birnin Lokoja, Kwamared Muhammad Inuwa Suleiman, ya ce sun fito ne don su nemi hakkinsu a wajen gwamnati kuma kamata ya yi gwamnati ta saurare su ba dakile su ba sakamakon matsalar tsadar rayuwa da ake ciki.
A nasa bangaren, shugaban kungiyar SSANU, Kwamred Muhammad Haruna ya ce wannan zanga-zangar itace mataki na karshe inda a yanzu zasu baiwa gwamnati wa’adin karshe, kuma idan ba’a dauki mataki ba zasu tsayar da ayyukan jami’o’in kasar gabadaya.
Kwamred Muhammad ya kuma kara da cewa, matakin da jami’an ‘yan sanda suka dauka na hana su fita tattaki daga dandalin Unity Fountain ya nuna rashin iya aiki ne karara.
Shi ma shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Joe Ajaero, ya zo da tawagarsa jim kadan bayan komawa dandalin Unity Fountain da shuwagabannin kungiyoyin SSANU NASU da JAC suka yi bayan zuwa ma’aikatun ilimi da na kwadago, inda ya yi Allah wadai da matakin da jami’an ‘yan sanda suka dauka a kan masu zanga-zanga yana mai cewa a fada wa kwamishinan ‘yan sandan birnin Abuja cewa idan ya kara yin yunkurin makamancin wannan, da ya sabawa doka zasu gudanar da zanga-zangar rufe ofishinsa.
Wannan dai ba shi ne karon farko da kungiyoyin 3 banda na ASUU ke fitowa zanga-zanga don mika koken su a game da rashin daidaito wajen kula da hakokkinsu ba.
A ranar 8 ga wannan watan sun sha alwashin gudanar da zanga-zanga a cikin jami’o’in gwamnati a fadin kasar.
Duk kokarin ji ta bakin bangaren jami’an tsaro a yayin hada wannan rahoton dai ya ci tura domin kuwa a yayin zanga-zangar ma sai da suka yiwa ‘yan jarida barazanar lalata kayan aikinsu.
Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:
Your browser doesn’t support HTML5