Jamhuriyyar Niger: Sababbin Jam’iyu Kusan 200 Ne Suka Yi Rijista

A jamhuriyar Nijer a yayinda ya rage ‘yan watanni a fara gudanar da zabubbuka, sababbin jam’iyun siyasa na ci gaba da bayyana a fagen siyasar kasar, inda bayanai ke nunin jam’iyu kusan 200 ne suka yi rijista a yanzu haka.

Mai rajiin kare dimokradiya, Nassirou Saidou na muryar Talakka ya ce, an samu koma bayan dimokradiya, bisa la’akari da yadda wasu ‘yan siyasa ke kokarin mayarda jam’iya tamkar wata masana’anta ko gurin saka jari.

Ya kara da cewa an mayar da siyasa kasuwanci, ya ce, yawaitar jam’iyyu da yawa ba al’kibla bace ta siyasa mai kyau.

Nassirou Saidou ya yi wadannan bayanan ne a wata hira da wakilin Muryar Amurka, Souley Moumouni Barma,

Saurari hirar:

Your browser doesn’t support HTML5

Jamhuriyyar Niger: Sababbin Jam’iyu Kusan 200 Ne Suka Yi Rijista