'Yan Sanda Sun Cafke 'Yan Fashi Da Makami 4 A Birnin Yamai

Hukumar ‘yan sandan jamhuriyar Nijar, ta yi nasarar cafke wasu ‘yan fashin da makami cikinsu har da wadanda suka hallaka wani direban tasi lokacin da suke kokarin kwace masa mota a wata anguwa a birnin Yamai.

Rukunin farko na ‘yan fashin da hukumar ‘yan sanda ta gabatarwa manema labarai ya kumshi matasa hudu, wadanda bincike akan kisan da aka yiwa wani direban tasi anan yamai a kwanakin baya ya rutsa da su, kamar yadda kakakin ‘yan sanda Kaftin Mainasara Adili Toro ke karin bayani.

Hukumar ta ‘yan sanda ta gabatar da wani rukuni na biyu na matasa daga cikin ‘yan fashin da dubunsu ta cika.

Tukin tasi a birnin yamai a wasu lokutan da sawu ya dauke aiki ne dake cike da hatsari, saboda haka shugaban kungiyar SyncoTaxi Gamatche, Mahamadou, ke jinjinawa hukumar ‘yan sandan sakamakon cafke wadanan ‘yan fashin.

Yawaitar amfani da miyagun kwayoyi a wurin matasa na daga cikin manyan dalilan da hukumar ‘yan sanda tace ta gano, suna jefa matasa cikin aiyukan asha a ‘yan shekarun nan, musamman a manyan birane.

Saboda haka hukumar tace dole ne a matsa kaimi wajen yaki da masu safarar miyagun kwayoyi, anan Jamhuriyar Nijer domin takawa wannan sabon al’amari burki.

Ga cikakken Rahoton daga wakilinmu Sule Mumuni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Jamhuriyar Nijar: Yan Sanda Sun Cafke Yan Fashi Da Makami 4 A Birnin Yamai