Kasar Nijar tare da hadin gwiwar wata kungiya ta kasar Faransa NOE, sun rattaba hannu a wata yarjejeniya na mika dajin Termit Tuntuma ga kungiyar, na tsawon shekaru Ashirin, dajin Termit na daya daga manyan dazuzuka masu kunshe da namun daji na Afirka.
A cewar Abdullahi Haruna, jagoran kungiyar NOE a Nijar, abunda yaja hankalinsu shine, wata kungiya da suka gani a kasar Cadi mai kula da daji goma sha shidda, babban burin su shine tattalin namun dajin dake neman bacewa.
Ya ci gaba da cewa, za su dauki matasan yankunan a horos da su aikin gandun daji, su gina rijijyoyi, kula da kiwon lafiya, inganta ilimi, yaki da masu fasa kwauri da yankin yayi kaurin suna da shi.
Game da cece kuce da jama'a ke yi kan cewar an sayar da dajin, ya ce sun dade suna ziyartar dajin tare da ganawa da hukumomin wajen, sarakunan gargajiya, masu aikin man fetur da sauran su, don neman shawarar su, aikin su kuma na inganta ci gaban al'umma ne.
Abdullahi ya tabbatar da cewa suna da isassun kayan aiki da suka hada da kanana jirage Drone kurman jirgin, lasifikoki da sauran su, don tabbatar da tsaro, hakan kuma ya ce zai janyo masu yawon buda ido daga wasu kasashen duniya.
Facebook Forum