Sojojin sun yi arangama da mayaka masu ikirarin jihadi a garuruwan Bague da Tchoungoua da ke yankin Diffa a ranar Alhamis, in ji majiyoyin.
“A bangarenmu, mun samu mutum biyu da suka samu kananan raunuka, kuma a bangaren mayakan, an kashe ‘yan Boko Haram biyar,” in ji Smain Younous, wanda aka nada a watan jiya a matsayin gwamnan Diffa.
Sojojin Nijar sun kwace bindigu AK-47 guda hudu daga hannun maharan.
Rikicin na ranar Alhamis ya biyo bayan kwanciyar hankali na ‘yan makonni a yankin Diffa, wanda a bana ma ya yi fama da mummunar ambaliyar ruwa daga kogin Yobe.
Kogin ya na da iyaka da Najeriya, inda ya ke tasowa kafin ya kwarara zuwa tafkin Chadi, wani yanki mai fadi da ke cike da tsibirai da fadama da ke zama mafaka ga kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Baya ga barazanar Boko Haram, Nijar kuma na fuskantar hare-hare akai-akai daga kungiyoyin’yan ta’adda na yankin Sahel, ciki har da kungiyar IS da ke yankin Sahara da ke yammacin kasar.
Yankin Diffa na dauke da ‘yan gudun hijira 300,000 ‘yan Najeriya da kuma ‘yan gudun hijira da rikicin Boko Haram da kungiyar IS ya tilasta su bar mazauninsu a yammacin Afirka, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Nijar wadda ita ce kasa mafi talauci a duniya bisa wani rahoton kididdigar ci gaban bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya, ta sha fama da tashe-tashen hankula da aka fara a arewacin Mali a shekarar 2012.