Tun farko dai kamfanin dillancin labarai na Reuters ne ya fitar da rahotan da ke cewa sojojin Najeriya sun kashe kananan yara a yakin da suke yi da masu tayar da kayar baya.
A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon ya sanyawa hannu, na cewa “Ma’aikatar tsaro ta damu kan da rahotan Reuters dake zargin takwarorinmu, kuma mun bi sahun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, na kira ga gwamnatin Najeriya da ta gudanar da bincike mai zaman kansa.”
Sanarwar ta kara da cewa, rundunar sojin Amurka ba ta da wani shiri na tsara zama da rundunar sojin Najeriya ko shugabanninsu a halin yanzu a taron kolin Amurka da Afirka da ke gudana a birnin Washington DC.
A daya bangaren kuma, da yake mayar da martini game da rahotan Reuters, karamin ministan raya kasa da Afirka na gwamnatin Birtaniya ya fadi ranar Talata cewa, rahoton da Reuters ya fitar na kashe kananan yara a yakin da suke yi da masu ta da kayar baya, abin damuwa ne matuka, kuma za a tabo batun Najeriya.
Mitchell ya ce Birtaniya za ta gabatar da batun ta bakin babban kwamishinanta a Abuja, babban birnin Najeriya.
Tun farkon fitowar rahotan na Reuters ake sukar sojojin Najeriya tare da kira ga gwamnatin kasar da ta gudanar da cikakken bincike don tabbatar da gaskiyar lamarin.
Rundunar sojin Najeriya ta ce ba za ta gudanar da bincike kan abin da ta ce ba shi da tushe ba.