Jamhuriyar Nijar: Mayakan Boko Haram Sun Kashe Mutane 38

Mutane na duba inda mayakan Boko Haram suka kai hari

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe a kalla mutane 38 a lokacin da suka kai wani hari kan wasu ‘kauyuka biyu a jamhuriyar Nijar,kusa da iyaka da Najeriya.

Wannan hari shine hari na kusa kusan nan da ‘yan Boko Haram suka kai kan kasashen dake makwabtan da juna da suka hada gwiwa da sojojin Najeriya domin dakile kungiyar ‘yan ta’addar.

A farkon satin nan ne dai jami’an kasar Chadi suka zargi kungiyar Boko Haram kan wasu harin kunar bakin wake har biyu da aka kai babban birnin kasar, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 33.

Kasar Chadi da Nijar da Kamaru, sun aika da sojojinsu a farkon shekarar nan domin yaki da ‘yan kungiyar.

A makon daya gabata ne kasashen suka kafa wata rundunar hadin gwiwa da cibiyar ta zata zamanto a N’Djemana babban Birnin kasar ta Chadi.

Kungiyar Boko Haram dai ta kafu ne a shekara ta 2009, tun daga nan ta kashe dubunnan mutane a Najeriya, ta harbin mutane da ma ‘dana boma bomai.

Gwamnatin najeriya dai ta kafa dokar ta baci a arewa maso gabashin kasar, bangaren da kungiyar Boko Haram ke aikata ta’addanci. Amma ba’a sami nasara ba.

A baya kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta zargi sojojin Najeriya, tana mai cewa an kashe karin fararen hula 8000 a fadan da ake yi da ‘yan Boko Haram.